Yadda Zaka yi Emergency Call batare da kacire Security ba



Assalamu Alaikum barka mu da warhaka da fatan kuna lafiya, 
Yau zanyi bayani ne akan yadda zaka yi kiran emergency waton kiran gaggawa, sau tari dayawa mukanyi cintuwar waya, ko kuma hadari bamu san security ba balle mukira yan uwan mai wayar, wani lokaci ma har sai an jira idan wani ya kira. To wannan damar ga masu aiki da 
smart phones ne mai suna Android.
Domin guje ma matsala mai kama da wannan muna bukatar natsuwa domin fahimtar yadda akeyi
  • Zaka shiga Setting din wayar ka sai kayi searching din "Emergency Information"
  • Bayan ka shiga zai nuna ma kamar haka 
  • Sai ka shiga Add contact bayan ka shiga zai nuna maka nambobi dake akan layin ka ko waya kamar haka 

  • Sai ka danna duk wanda kake kana iya adding har mutun goma, zakaga nayi adding din mutun biyu a hoto na kasa

  • bayan haka sai ka rufe wayar waton kabari ya shiga security 

Yadda  Ake Amfani Dashi 
  • kafin kacire security zaka ga inda akasa "Emergency" sai ka danna shi zai nuna ma haka 

  • Anan ana bukatar ka danna wannan inda arow ke nuna ma da sauri koda sau ukku ne
  • Baya Kayi haka zai nuna ma mutanen da kayi adding kamar haka 
    Kaga mutum biyu da nayi adding daga contact dina zan iya kiran su batareda na cire security ba hakama duk lokacin da wani yayi tsintuwar wayar zai iya kiransu ba tareda ya cire security ba."

Haza Wassalam

0 Comment:

Post a Comment